Isa ga babban shafi

Biden ya amince da ci gaba da zaman sojin Amurka a Somalia

Shugaba Joe biden na Amurka ya amince da sake zaman dakarun kasarsa a Somalia don ci gaba da yakar 'yan kungiyar Al-Shabab mai ikrarin jihadi da ke da alaka da Alqa’ida.

 Shugaban Amurka, Joe Biden
Shugaban Amurka, Joe Biden AP - Manuel Balce Ceneta
Talla

Kusan watanni 18 bayan janyewar sojojin Amurka 750 da aka jibge a wannan kasa da ke kahon Afirka, wanda tshohon shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarni a karshen wa'adinsa, yanzu haka kasa da sojojin Amurka 500 na musamman ne za a jibge a Somaliar, kamar yadda jami’in da ya bukaci a sakaya sunansa ya baiyana, ba tare da bayyana ranar saukar dakarun ba.

Biden ya amince da bukatar da Ma'aikatar Tsaro ta gabatar ta mayar da dakarun Amurka a gabashin Afirkar, don sake kafa wani karamin sansanin sojin a kasar ta  Somalia, kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Shugaba Biden ya ci gaba da cewa ya dauki wannan mataki ne don inganta harkokin tsaro da nuni da zakakurancin dakarun na musamman da suka shafe sama da shekara guda tun a gwamnatin da ta gabata a Amurka da ta yanke shawarar tura dakarun Somalia don yakar ta’addaci  a kasar.

Donald Trump ya ba da umarnin ne a watan Disambar shekarar 2020, kafin karshen wa'adinsa, game da janye sojojin Amurka daga Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.