Isa ga babban shafi

Tashin farashin kayaki ya jefa mutane miliyan 71 a matsanancin talauci

Hauhawar farashin abinci da makamashi a duniya ya jefa mutane miliyan 71 cikin talauci, galibi a matalautan kasashe a cewar wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, yayin da karuwar talauci a kasashe masu tasowa a cikin watanni uku da suka gabata ya yi kamari fiye da lokacin cutar COVID-19.

Talauci na karuwa a sassan Afrika galibi kasashen da ta'addanci ke tsanata.
Talauci na karuwa a sassan Afrika galibi kasashen da ta'addanci ke tsanata. REUTERS/Joe Penney
Talla

Don magance wannan batu, Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akwai bukatar a tantance gidajen ko kuma magindatan dake cikin wani hali tare da tura musu kudade, yayin da ta ce gwamnatocin za su bukaci tallafi daga bangarori daban-daban domin samun biyan bukata.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma yi gargadin cewa, yayin da manyan bankunan kasashe ke kara kudin ruwa don magance hauhawar farashin kayayyaki, akwai yuwuwar kara haifar da koma bayan tattalin arziki da zai kara ta'azzara matsalar, tare da kara habaka talauci a duniya.

Rahoton ya yi nazari kan kasashe 159, inda ya gano cewa lamarin ya fi kamari a yankin Balkan, da yankin tekun Caspian da kuma yankin kudu da hamadar Sahara, musamman a yankin Sahel.

Daga cikin kasashen da ke fuskantar matsalar tashin farashin kayayyaki, a cewar rahoton, akwai Armenia, Uzbekistan, Burkina Faso, Ghana, Kenya, Rwanda, Sudan, Haiti, Pakistan, Sri Lanka, Habasha, Mali, Najeriya, Saliyo, Tanzaniya da Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.