Isa ga babban shafi
WHO-Bankin Duniya

Mutane miliyan 500 za su fada tsananin talauci saboda corona- rahoto

Wani rahoton hadin gwiwa tsakanin hukumar lafiya WHO da Bankin Duniya ya nuna yadda cutar covid-19 ta haddasa gagarumar matsala ta fuskar ci gaba da kuma koma bayan akalla shekaru 20 wanda ya kai ga jefa mutane fiye da miliyan 500 cikin matsanancin talauci dai dai lokacin da jama'a ke fuskantar matsala da kuma tsadar kula da lafiya.

Wani yanki na Yemen da talauci ya tagayyara.
Wani yanki na Yemen da talauci ya tagayyara. - AFP
Talla

Yayin bikin ranar lafiyar al'umma na bana mai taken mummunar tasirin Covid-19, bangarorin biyu sun sake fayyace kololuwar matsalar da annobar ta covid-19 ta jefa Duniya musamman ta fuskar ci gaba.

Rahoton hukumomin biyu ya buga misali da yadda cutar ta covid-19 ta yi kokarin gagarar bangaren lafiyar hatta kasashen da suka ci gaba a shekarar 2020, duk da kokarin shawo kan annobar.

Sabon rahoton na WHO da Bankin Duniya ya kuma yi gargadin kan yadda matsalolin tattalin arziki ke ci gaba da tsananta a bangare guda kuma al'umma ke kara talaucewa saboda katsewar hanyoyin samu da kuma tsadar rayuwa baya ga gazawar gwamnatoci.

Acewar WHO kafin covid-19 kashi 68 cikin 100 na al'ummar duniya sun samu sassaucin kiwon lafiya, musamman bangaren kula da mata masu juna biyu da ayyukan rigakafi da yaki da cutukan HIV da tarin TB da ma saukin magungunan cutuka marasa yaduwa irin su daji, ciwon zuciya da kuma ciwon sukari.

Sai dai rahoton hukumomin biyu ya ce, bullar covid-19 ta tsawwala harkokin kula da lafiya wanda zai zamewa mutane gagarumar matsala a yanzu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.