Isa ga babban shafi
WHO-Omicron

Nau'in corona na Omicron ya fantsama kasashe 57 - WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a halin yanzu sabuwar nau’in cutar covid19 da aka fi sani da omicron ta shafi kasashe 57 a duniya, a daidai lokacin da kamfanonin BioNTech da Pfizer ke cewa bayar da allurar rigakafin COVID-19 sau uku na kawar da sabon nau’in cutar ta Omicron.

WHO dai ta ce nau'in na Omicron ba shi da hadarin da ake hasashe.
WHO dai ta ce nau'in na Omicron ba shi da hadarin da ake hasashe. Justin TALLIS AFP/File
Talla

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhenum Ghebreyesus da yayi sanarwar a wani taron manema labarai jiya laraba, ya shawarci Kasashe su kaucewa nuna banbance banbance wajen haramtawa masu tafiye tafiye shiga kasashensu.

Shugaban ya ce akwai alamomi da dama dake nuna kwayar cutar Omicron, misali yadda cutar ke yaduwa tamkar wutar daji a fadin duniya, abinda ke nuni da cewa yana iya yin babban tasiri a kan yadda annobar take.

Ghebereyesus ya kuma bukaci Kasashe su sake nazartar shirye sahiryensu, ta hanyar gaggauta yi wa al’umar dake cikin hatsari rigakafi, kara inganta harkokin kiwon lafiya, sa ido tare gudanar da gwaje gwaje da duk wanda ake zargi da nuna alamomin harbuwa da cutar, dan hana cigaba da yaduwar cutar.

A kiran da yayi wa Kasashe, Gheberayesus ya ce, kwayar cutar ta omicron na canza salon tafiya, dan haka kada ayi kasa a gwiwa, a kuma hada karfi da karfe wajen dakile cigaba da yaduwarta, kazalika a yi duk mai yiwuwa wajen hana wasu sabbin nau’in cutuka tasowa, toh tabbas za’a a iya hana Omicron zama matsalar da ta shafi duniya.

Shugaban ya kuma jinjinawa wasu Kasashe da suka hada da faransa da Switzerland da suka daga takunkumin hana ‘yan Afrika ta kudu shiga kasarsu, saidai yayi kira ga al’umma su cigaba da mutunta shawarwarin hukumomin kiwon lafiya na bada tazara tsakanin juna, yawan wake hannuwa, yin amfani da takunkumin rufe hanci, kauracewa taro ko dandazon mutane da dai sauransu, dan hana cigaba da yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.