Isa ga babban shafi
Corona-Omicron

Hadarin nau'in corona na Omicron bai zarta na Delta ba- WHO

Kwararru daga Amurka da hukumar Lafiya ta Duniya sun ce sabon nau’in corona na Omicron ba shi da wani banbancin barazana idan aka kwatantashi da sauran nau’ikan da suka gabata kamar na Delta da sauransu. Kalaman dai ya wanke shakku da kuma rudanin da Duniya ta shiga na yiwuwar sabon nau’in ya iya kasancewa mafi hadari.

Shugaban sashen agajin gaggawa na WHO Michael Ryan.
Shugaban sashen agajin gaggawa na WHO Michael Ryan. Fabrice COFFRINI AFP
Talla

Kalaman kwararrun ya kawar da shingen da ya haddasa fargaba kan yiwuwar sabon nau’in na Omicron ya dara wadanda suka gabace shi ta fuskar hadari, dalilin da ya sanya kasashe daukar matakan tsaurarawa har ma da rufe iyakoki don kare al’ummominsu.

Shugaban sashen agajin gaggawa na WHO Michael Ryan ya ce bincikensu bai nuna musu nau’in na Omicron na da wani hadari na musamman ba, sabanin hasashen da was uke yi.

Sai dai a jawabin Ryan, jami’in ya sanar da cewa za su ci gaba da bincike kan sabon nau’in na Omicron don sake samun nutsuwa kan illar da ka iya yiwa jama’a dai dai lokacin da wasu daga cikin kamfanonin samar da rigakafin cutar ciki har da hadakar Pfizer da BioNTech ke cewa nasu nau’in rigakafin na da tasiri kan nau’in na Omicron, idan aka karbi allurai guda 3.

Kalaman kwararrun na zuwa dai dai lokacin da bangare guda hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin Duniya ke gargadi kan tilastawa jama’a karbar rigakafi, bayan da hukumomin kasashe a baya-bayan nan suka dauki matakin tilascin musamman bayan bayyanar nau’in Omicron mai saurin yaduwa.

Cikin wani sakon bidiyo da shugabar hukumar Michelle Bachelet ta fitar ta bukaci kasashe su mutunta dokokin kare hakkin dan adam gabanin tilastawa al’ummominsu karbar rigafin na covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.