Isa ga babban shafi
ANNOBAR-KORONA

Hukumar Lafiya tace an samu Omicron a kasashe 38

Hukumar Lafiya ta Duniya tace ya zuwa yau juma’a an samu bullar cutar korona nau’in Omicron a kasashe 38, amma kuma babu koda mutum guda da aka sanar ya mutu saboda ita.

Daraktar Hukumar Lafiya Maria van Kerkhove
Daraktar Hukumar Lafiya Maria van Kerkhove AP - Martial Trezzini
Talla

Daraktar Hukumar Maria Van Kerkhove tace cutar ta karade nahiyoyin duniya guda 6 da ake da su, kuma zai dauki makwanni kafin fahimtar illar nau’in Omicron da samar masa da magani da kuma yadda za’a kula da wadanda suka harbu.

Hukumar tace masana kimiya a kasashen duniya na can suna raba dare domin gudanar da bincike akan sabon nau’in da zummar samarwa duniya mafita.

Kakakin Hukumar Lafiyar Michael Ryan yace nan bada dadewa ba zasu samar da amsoshin tambayoyin da mutanen duniya keyi game da cutar, kuma yana da muhimmanci a amince da tasirin kimiya da kuma yin hakuri da yanayin da ake ciki, maimakon nuna fargaba.

Van Kerkhove tace akwai shawarwarin dake bayyana cewar nau’in Omicron na saurin yaduwa, amma zai dauki kwanaki kafin samun Karin haske akai.

Hukumar Lafiyar ta bukaci jama’a da su ci gaba da karbar allurar rigakafin da ake bayarwa domin kare lafiyar su da na sauran jama’a

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.