Isa ga babban shafi
ANNOBAR-KORONA

Hukumar Lafiya tace babu wanda ya mutu sakamakon harbuwa da Omicron

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu ba ta samu wani rahoton wani da ya mutu ba sakamakon sabon nau’in cutar korona ta Omicron, sai dai ta ce tana tattara bayanai game da nau’in cutar da aka samu, yayin da kasashe ke jan hankalin akan yadda za a hana ta yaduwar ta a sassan duniya.

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus Christopher Black World Health Organization/AFP/File
Talla

Kakakin hukumar lafiya ta WHO Christian Lindmeier ya shaidawa manema labarai a Geneva cewar, har yanzu suna tattara bayanai ne akan halin da kasashe ke ciki, da kuma yadda za a sake bullo da sabbin matakan kariya domin dakile yaduwar ta.

A cewar sa, kasashe da dama na ci gaba da yiwa al’ummominsu gwajin sabon nau’in cutar, haka kuma kamar yadda kwararru a fannin cututtuka masu yaduwa suka yi gargadi, hakan ta sanya hukumomi daukar matakan taka tsan-tsan.

Yayin da nau’in Omicron ya harzuka duniya, Lindmeier ya kuma bukaci mutane da su kula da na’u’in Delta, wanda ke da kashi 99.8 na samfurin da aka mikawa shirin kimiyyar duniya na GISAID a cikin kwanaki 60 da suka gabata.

Jami’in ya kara da cewa Omicron na iya yaduwa fiye da tsammani, inda ake fargabar tarin kalubalen da zai iya haifarwa, to amma abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai yanzu shine, wannan nau’in na Delta.

Lindmeier ya ce dokokin da aka tsaurara a wasu kasashen makonni biyu da suka gabata, musamman rufe harkokin kasuwanci, dokar kulle a wasu yankuna da rufe kasuwannin kirsimeti a yankin Turai, idan aka tuna, an yi su ne kafin zuwan Omicron, wato lokacin da nau’in Delta ke mamaya, saboda haka kada ayi kasa a gwiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.