Isa ga babban shafi
Coronavirus

WHO ta yi gargadi kan tilastawa jama'a karbar rigakafin covid-19

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta gargadi hukumomi kan tilastawa jama'a karbar allurar rigakafin Covid-19, ta na mai kiran cewa abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne bayar da cikakkiyar kariya musamman ga kananan yara, la’akari da yadda su ke da garkuwa mai rauni.

Daraktan hukumar Lafiya ta Duniya mai kula da nahiyar Turai Hans Kluge.
Daraktan hukumar Lafiya ta Duniya mai kula da nahiyar Turai Hans Kluge. Alexander Astafyev Sputnik/AFP/Archivos
Talla

Daraktan hukumar ta WHO mai kula da nahiyar Turai Hans Kluge ya ce tilasta karbar rigakafin ya kamata ya zama mataki na karshe kuma za a iya amfani da shi ne kawai idan duk wasu matakan da aka samar sun gaza cimma abin da ake fata.

WHO ta ce maimakon umarnin da hukumomi suka bayar na karbar rigakafin a wasu wuraren, ya kamata a karfafawa jama’a gwiwa da kuma cire musu shakku, maimakon a tilasta musu.

Hukumar ta lafiya ta kuma lura cewa adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu da adadi mai yawa, kama daga tsoffin da masu matsakaitan shekaru zuwa kananan yara, wanda hakan ke nuna cewa umarnin da aka bayar akwai alamar tambaya a kai.

Kluge ya ce, yara ne suka fi hadarin kamuwa da cutar a halin yanzu, kuma ana fargabar ma su yadawa iyaye ko kuma kakanninsu a gida.

WHO ta nanata cewa ya kamata a tsaurara dokar amfani da takunkumin rufe fuska a makarantun firamare, amma kumata hanyar wayarwa da daliban kai muhimmancin amfani da shi, domin kaucewa fadawa gidan jiya, na rufe makarantu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.