Isa ga babban shafi

Saudiyya ta yi maraba da kisan jagoran al-Qaeda Ayman al-Zawahiri

Ma’aikatar harkokin wajen Saudi Arabia ta yi maraba da kisan da Amurka ta yiwa shugaban kungiyar al-Qaeda Ayman al-Zawahiri, wanda hukumomi suka shafe tsawon lokaci suna nema ruwa a jallo sakamakon hannunsa a kitsa harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 ko kuma 9/11.

Jagoran kungiyar al-Qaeda Ayman al-zawahiri.
Jagoran kungiyar al-Qaeda Ayman al-zawahiri. AFP - -
Talla

Sanararwar ma’aikata harkokin wajen ta Saudiyya na zuwa ne jim kadan bayan sanarwar da shugaba Joe Biden na Amurka da ke ikirarin cewa a wani samame ne da ta kai da jirgi mara matuki, Amurka ta kashe Zawahiri, daya daga cikin ‘yan ta’addan da aka fi nema ruwa a jallo a duniya.

Shugaba Joe Biden a jawabinsa na asubahin yau talata ya ce Amurka ta yi nasarar kisan jagoran ne a hare-haren da hukumar CIA kai da jiragen yaki kan maboyar mayakan na al-Qaeda da ke birnin Kabul na Afghanistan.

A cewar Joe Biden a lahadin da ta gabata ne dakarun na ta suka kaddamar da farmakin a babban birnin na Afghanistan. 

Zawahiri wanda kwararren Injiniya ne ya karbi jagorancin kungiyar al-Qaeda ne a shekarar 2011, bayan mutuwar Osama bin Laden, wanda aka yi amannar tare suka kitsa harin na ranar 11 ga watan Satumban 2001 ko kuma 9/11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.