Isa ga babban shafi

Pelosi ta yi biris da barazanar China kan ziyarar Taiwan

Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta isa Taiwan a yammacin wannan Talatar, inda ta yi biris da gargadi da kuma barazanar da China ta yi, lamarin da ya haifar da mikewar jijiyoyin wuya tsakanin manyan kasashen biyu.

Pelosi a Taiwan
Pelosi a Taiwan AFP - HANDOUT
Talla

Pelosi, ita ce ta farko a jerin manyan jami’an Amurka masu rike da mukaman siyasa da ta ziyarci Taiwan a cikin shekaru 25 da suka gabata, yayin da China ta ce, tana kallon wannan ziyarar tamkar takalar fada da kuma jefa yankin cikin fargaba.

Hotunan talabijin da aka watsa kai-tsaye sun nuna yadda Pelosi mai shekaru 82 ta sauka Taiwan a cikin jirgin sojin Amurka, inda aka rika yi mata gaisuwar ban-girma da lale marhabin a filin jiragen sama na Songshan da ke Taipei.

Jim kadan da isarta Taiwan din, Pelosi ta fitar da wata sanarwa da ke cewa, ziyararta ta nuna yadda Amurka ke jajircewa wajen nuna goyan baya ga tsarin demokuradiyar Taiwan, tana mai cewa, wannan sada zumuncin bai ci-karo da manufar Amurka kan Taipei da Beijing ba.

Tuni ita ma Taiwan ta bayyana ziyarar a matsayin karfafa goyon baya da ta samu daga Washington.

A bangare guda, bayanai na baya-bayan nan na cewa, rundunar sojin China na cikin shirin ko-ta-kwana kuma da yiwuwaar ta kaddamar da jerin hare-hare kan duk wani yunkuri na soji a matsayin martani kan ziyarar ta Pelosi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.