Isa ga babban shafi

Pelosi na ziyara a kasashen Asiya amma babu tabbas kan zuwa Taiwan

Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi za ta jagoranci tawagar majalisar zuwa yankin Asiya da tekun Pasifik, kamar yadda ofishinta ya tabbatar ranar Lahadi, inda rangadin zai kaita zuwa kasashen Singapore da Malaysia da Koriya ta Kudu da kuma Japan.

Kakakin Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi tana magana yayin taron manema labarai na mako-mako a kan Capitol Hill a Washington, Amurka Janairu 20, 2022.
Kakakin Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi tana magana yayin taron manema labarai na mako-mako a kan Capitol Hill a Washington, Amurka Janairu 20, 2022. REUTERS - POOL
Talla

Sanarwar ba ta bayyana ko tawagar mai wakilai 6 za ta ziyarci kasar Taiwan ba, wani batu da Amurka da China suka tattaunawa kan shirin ziyarar.

Sanarwar da ofishin Pelosi ya fitar ta ce, "ziyarar za ta mayar da hankali ne kan harkokin tsaro da hadin gwiwar tattalin arziki da kuma tabbatar da  mulkin dimokradiyya a yankin IIndia da tekun Pacific."

Tawagar na jam’iyyar Democrat ta kunshi shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar Gregory Meeks da mambobin kwamitin dindindin na majalisar wakilai kan leken asiri da kwamitin ayyukan soja na majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.