Isa ga babban shafi

Jirgin ruwa makare da hatsi ya isa Turkiya daga Ukraine karon farko a watanni 5

Jirgin farko makare da hatsi daga Ukraine ya isa gabar ruwan Turkiya inda tuni jami'an tashar jiragen ruwan suka duba tare da tabbatar da abin da ke kunshe, wanda ke zuwa karkashin wata mahimmiyar yarjejeniya da ke son ganin Rasha ta janye sojojin ruwanta daga hanyar da ta datse.

Da safiyar yau jirgin ya isa Turkiya wanda ke matsayin na farko da ya bar tashar ruwan Ukraine cikin watanni 5.
Da safiyar yau jirgin ya isa Turkiya wanda ke matsayin na farko da ya bar tashar ruwan Ukraine cikin watanni 5. AFP - OZAN KOSE
Talla

Jirgin wanda ya tashi karkashin wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin majalisar dinkin duniya da Turkiya da zummar fitar da dimbim tan-tan na hatsi da suka makale a Ukraine don magance matsalar karancin abinci da ta kunno kai a duniya a safiyar yau ne ya isa Istanbul dauke da tutar Sierra Leone.

Jirgin ya isa gabar ruwan Bosphorus Strait ne jim kadan bayan da Ukraine ta sanar da fara kwashe fararen hula daga yankin Donetsk da ke shan luguden wuta ba kakkautawa daga Rasha, wanda ke matsayin irinsa na farko cikin watanni 5 da ya iso gabar ruwan daga Ukraine bayan fara mamayar Moscow.

Matakin Rashan na sanya sojoji akan ruwa da ya hana fitar da hatsi daga Ukraine ya jefa duniya a halin kunci da yunwa saboda karanci da kuma tsadar abincin da ake fuskanta a watanni 5 da suka gabata.

Kasashen na Rasha da Ukrain na matsayin 'yan gaba-gaba da ke wadata Duniya da alkama wanda kuma yakin bangarorin ya zama silar karanci da kuma tsadarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.