Isa ga babban shafi

Kotun Amurka ta aike da Mijin Nancy Pelosi gidan yari saboda tuki cikin maye

Kotu a Amurka ta aike da mijin shugabar Majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi gidan yari na kwanaki 5 sakamakon samun shi da laifin tuki bayan mankas da barasa da ya kai shi ga hadari tun a watan Mayun da ya gabata. 

Shugabar Majalisar wakilan Amurka.
Shugabar Majalisar wakilan Amurka. REUTERS - ELIZABETH FRANTZ
Talla

Paul Pelosi mai shekaru 82 wanda ya yi hadari da motarsa kirar Porsche a yankin Napa County da ke birnin California a ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata, sakamakon mankas da barasa, tuni ya amsa laifinsa gaban kotu.

Yayin yanke hukunci, alkalin da ya jagoranci shari'ar ya ce saboda da'ar da Mr Paul Pelosi ya nuna gaban shari'a an yafe masa kwanaki 2 na hukuncin yayinda kwana guda da ya yi a hannun jami'an tsaro ranar da hadarin ya faru zai kasance a madadin hukuncin kwanaki 2 yayinda sauran kwana guda kuma alkalin ya umarci Mr Pelosi da ya gudanar da ayyukan taimakon jama'a na tsawon sa'o'i 8.

Kotu dai bata samu Mr Paul Pelosi da aikata wani laifi makamancin tuhumar ba dalilin da ya sanya shi fuskantar sassaucin hukunci.

Sai dai karkashin shari'ar Mr Pelosi wanda ke da kamfanin venture capital firm zai biya tarar dala dubu 7 amma hukuncin bazai sanya shi asarar lasisin tukinsa ba.

Yayin hukuncin na jiya talata dai ba a ga fuskar Mr Pelosi a dakin shari'ar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.