Isa ga babban shafi

MDD ta kai ziyara cibiyar nukiliya ta Zaporizhzhia da ke hannun Rasha

Tawagar kwararun hukumar kula da makamashin nukliya ta duniya, (AIEA) ta ce, za ta ci gaba da tsayawa a cibiyar nukliya ta Zaporizhzhia da ke Ukraine,  bayan da ta kai wani rangadi, domin kaucewa faruwar hadarin nuliya ga cibiyar, a dai dai lokaci da  kasashen Rasha, da Ukraine ke zargin juna da kai hare hare a wannan wuri.

Cibiyar nukiliya mafi girma a Turai ta Zaporizhzhia da ke yankin Enerhodar a Ukraine
Cibiyar nukiliya mafi girma a Turai ta Zaporizhzhia da ke yankin Enerhodar a Ukraine REUTERS - Alexander Ermochenko
Talla

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya bayyana cewa, ziyarar tawagar a cibiyar nukiliyar Zaporizhzha da ke hannun Rasha a kudancin Ukraine, zai ci gaba da kasancewa har zuwa ranar Lahadi ko Litinin.

Rafael Grossi, wanda ke jagorantar tawagar binciken ya ce, akwai wata tawaga da za ta kasance a wurin har zuwa Lahadi ko Litinin, tare da ci gaba da tantance halin da ake ciki.

Rahotanni na cewa tawagar mutum 14 suka isa kasar ta Ukraine karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai jagoran tawagar, bai bayyana adadin mutanen da za su zauna a wurin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.