Isa ga babban shafi

Faransa ta yi watsi da zargin da ake yi wa sojinta a kisan Rwanda

Alkalan Faransa sun yi watsi da tuhumar da ake yi wa wasu sojojin kasar kan zargin su da hannun a kisan kare-dangin da ya auku a shekara ta 1994 a Rwanda.

Kasusuwan kwarangwal na mutanen da aka yi wa kisan kare dangi a Rwanda
Kasusuwan kwarangwal na mutanen da aka yi wa kisan kare dangi a Rwanda AFP
Talla

Wasu ‘yan Rwanda da suka tsira daga kisan kiyashin na 1994, su ne suka zargi sojojin na Faransa da aka girke a kasar a wancan lokacin da yin sakaci da gan-gan har mayakan Hutu suka yi wa daruruwan ‘yan uwansu daga kabilar Tutsi kisan gilla a yankin Bisesero da ke yammacin kasar.

Tun a cikin watan Disamban 2005 ne, masu shigar da kara na gwamnatin Faransa suka fara gudanar da bincike kan yiwuwar hadin-baki da sojojin wajen aikata laifukan yaki bayan da mutanen da suka tsira da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun shigar da kara.

Sai dai daga bisani alkalan na Faransa sun gaza tantance gaskiyar zargin da ake yi wa sojojin kasar na hannu kai-tsaye a kisan kare-dangin na Rwanda kamar yadda wata sanarwar da suka fitar ta ce.

Ko a bara, sai da masu bincike kan lamarin suka bukaci a yi watsi da wannan shari’ar.

Faransa wadda ta samu kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan Hutu a wancan lokaci, ta aike da dubban sojojinta zuwa kasar ta Rwanda karkashin wani aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.