Isa ga babban shafi

Putin ba zai halarci jana'izar Sarauniya Elizabeth ba- Kremlin

Fadar Kremlin ta fitar da sanarwar cewa, Shugaba Vladimir Putin ba zai samu damar halartar jana’izar Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth ta biyu da ta mutu a jiya alhamis ba.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. AP - Alexey Maishev
Talla

A jawabinsa gaban manema labarai, mai magana da yawun shugaba Putin, Dmitry Peskov ya amsa tambaya game da yiwuwar halartar shugaban jana’izar Sarauniya, inda ya kada baki ya ce sam babu wannan shirin a kasa.

Dmitry Peskov ya bayyana cewa duk da yadda Sarauniyar ke da matukar muhimmanci da kima ga shugaba Putin amma yanayi ba zai bas hi damar halartar jana’izar ba.

A jawabinsa jiya alhamis jim kadan bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth shugaba Putin ya bayyanata a matsayin jajirtacciya da ta samar da ci gaba mai dorewa.

Ba kadai Putin ba al’ummar Rasha a hukumance ta gudanar jimamin mutuwar sarauniyar mai shekaru 96 wadda ta shafe shekaru 70 akan kujerar sarauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.