Isa ga babban shafi

Iyalan sarauniya Elizabeth sun taru a Balmoral cikin damuwa game da lafiyarta

Fadar Buckingham ta sanar da cewa likitoci na halin matukar damuwa game da lafiyar Sarauniya Elizabeth ta 2 dalilin da ya sanya ajje tarin jami’an lafiya a kusa da basarakiyar.

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II AFP - JONATHAN BRADY
Talla

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta 2 mai shekaru 96 na fama da rashin lafiya ne tun cikin watan Oktoban bara wanda ke bata matsala wajen iya tafiya ko kuma tsayuwa akan kafafuwanta na tsawon lokaci.

Fadar ta Buckingham a sanarwar da ta fitar da ranar yau alhamis ta ce, Sarauniyar ta Ingila ta fi samun nutsuwa a ci gaba da zama a fadarta da ke Scotland, tun bayan bikin cikar ta shekaru 70 a karagar mulki.

Wasu bayanai da fadar ta Buckingham ta fitar ta ce ilahirin iyalan gidan sarautar yanzu haka sun tattaru a Scotaland. 

Tuni dai hankulan al’ummar Birtaniya ya tashi game da rashin Sarauniyar inda Firaminista Liz Truss a wani sako da ta wallafa a Twitter ta ce dukkanin al’ummar kasar na cikin damuwa game da rashin lafiyar sarauniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.