Isa ga babban shafi

Kasashen yamma na zargin Belarus da hada kai da Rasha

Kungiyar G7 ta kasashe masu karfin tattalin arziki ta ce, shirin shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko na tura dakarun hadin gwiwa da Rasha wani sabon misali ne na hada kai da Moscow, tana mai gargadin gwamnatin Minsk da ta daina goyon bayan yakin Vladimir Putin a Ukraine.

Shugabannin kasashen na duba yuwuwar daukar mataki kan Belarus
Shugabannin kasashen na duba yuwuwar daukar mataki kan Belarus © wikipedia
Talla

Sanarwar da rundunar sojin hadin gwiwa da Rasha ta fitar ya zama misali na baya-bayan nan na yadda gwamnatin Belarus ke yin hadin gwiwa da kasar Rasha, a cewar shugabannin G7 ta cikin wata sanarwa da suka fitar, inda suka bukaci gwamnatin Lukashenko da ta mutunta hakkinta na dokokin kasa da kasa.

Gwamnatin Minsk ta ce wata tawaga na sojojin Belarus da ke jibge tare da sojojin Rasha rukuni ne na kariya kawai wanda manufar ita ce kare iyakokin tsohuwar jamhuriyar Soviet mai alaka da Rasha.

A farkon makon nan ne shugaban Belarus Alexander Lukashenko, wanda ke zama na hannun daman shugaban Rasha Vladimir Putin, ya sanar da cewa kasashen sun jibge sojojin hadin gwiwa, amma bai bayyana inda suke ba.

Ya ce kafa wadannan dakaru ya zo daidai da fashewar wani abu a wata gadar da ta hada yankin Crimea da Rasha, alhakin da Moscow ta dora a kan Ukraine.

Wannan tura sojojin ya haifar da fargabar cewa sojojin Belarus za su iya hada kai da sojojin Rasha a fafutukar da kasar ke yi na kwace da kuma rike wasu yankuna a gabashin Ukraine.

Sai dai shugaban kwamitin tsaro na Belarus Alexander Volfovich ya ce wannan cece-kucen be dace ba, kuma ya ce kasashen yammacin duniya suna tunanin kai wa Belarus hari bisa wannan dalili.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.