Isa ga babban shafi

Yan jam'iyya mai mulki a Indiya sun kona hotunan ministan harakokin wajen Pakistan

Mambobin jam'iyya mai mulki a Indiya sun kona hotunan ministan harakokin wajen Pakistan a yau asabar, bayan yakin caccar baki tsakanin 'yan hamayyar kudancin Asiya a Majalisar Dinkin Duniya.

Tarzoma tsakanin yan India da Pakistan
Tarzoma tsakanin yan India da Pakistan REUTERS - STRINGER
Talla

Pakistan da ke da makamin nukiliya ta lalata dangantakarta da dama tun bayan samun 'yancin kai daga Biritaniya shekaru 75 da suka gabata.

A wannan makon a Majalisar Dinkin Duniya a New York, Ministan harakokin wajen Indiya  Jaishankar ya gaya wa Pakistan cewa "kokarin zama da makwabci nagari" na da tasiri, yana mai kiran kasar Pakistan a matsayin "tushen ta'addanci".

Takwaransa na Pakistan Bilawal Bhutto Zardari ya mayar da martani inda ya kira Firayim Ministan Indiya Narendra Modi mai kishin addinin Hindu "mai yankan Gujarat".

Wannan na zuwa ne a lokacin da Modi ya kasance babban ministan jihar Gujarat lokacin da tarzomar addini a shekarar 2002 ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 1,000 galibinsu musulmi. An zarge shi da rufe ido.

A ranar Juma'a daruruwan mambobin jam'iyyar Modi ta Bharatiya Janata Party (BJP) sun gudanar da zanga-zanga a wajen babban hukumar Pakistan a New Delhi saboda kalaman.

BJP ta sanar da sabbin zanga-zanga a fadin kasar a yau asabar, kuma a biranen Bhubaneswar, masu zanga-zangar Amritsar da Ranchi sun kona hotunan Bhutto Zardari tare da rera taken.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.