Isa ga babban shafi

Majalisar dokokin Amurka ta zargi Donald Trump da cin amanar kasar

Kwamitin da ke binciken harin da aka kai a Majalisar Dokokin Amurka a bara ya ba da shawarar a tuhumi Donald Trump da laifuffuka da suka hada da tayar da kayar baya a binciken da ka iya jefa tsohon shugaban a gidan yari.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump kenan
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump kenan © Rebecca Blackwell / AP
Talla

Kwamitin da aka zaba na majalisar wakilai ya bukaci a gurfanar da shi, da kuma tuhumar da ake masa na dakile wani aiki a hukumance da kuma hada baki da zamba a Amurka bayan wani bincike na tsawon watanni 18 kan hargitsin Majalisar na ranar 6 ga Janairun, 2021.

Akalla mutane biyar ne suka mutu bayan da wasu gungun ‘yan zanga-zanga suka yi bore da sunan anyi wa Trump magudi a zaben da aka yin a awncan lokaci, kuma shugaban da ya sha kaye ya umurce su da su yi tattaki zuwa Majalisa, abin da ya sanya suka mamaye kujerar mulkin dimokuradiyyar Amurka a wani yunkuri na hana mika mulki ga shugaba Joe Biden. .

Kwamitin bangarorin biyu dai ya kada kuri'ar amincewa da mika tuhume-tuhumen ga ma'aikatar shari'a bayan bude jawabin da mataimakiyar shugaban kwamitin Liz Cheney ta yi, inda ta zargi Trump da yin watsi da aikinsa na rashin yin gaggawar yunkurin dakatar da tarzomar tare da bayyana shi da cewa bai dace da kowane mukami ba.

Har ila yau, wani babban koma baya ne ga Trump a cikin ‘yan makonnin da suka gabata tun bayan da ya sanar da sake neman takarar shugabancin Amurka, ciki har da zaben tsakiyar wa’adi na ‘yan Republican.

Zarge-zarge na iya haifar da dakatarwa daga shiga ofishin gwamnati ga tsohon shugaban mai shekaru 76, wanda har yanzu yana da iko sosai a jam'iyyar Republican, ko da kuwa ya shiga kurkuku.

Masu bincike sun ce rikicin ya fara ne tun daga yakin neman zaben Trump bayan yada zarge-zargen cewa ana kokarin shirya magudi a zaben.

Ana zarginsa da kokarin bata kimar ma'aikatar shari'a da kuma tursasa mataimakinsa Mike Pence, da jami'an zabe da 'yan majalisar dokoki da su yi watsi da zaben ta hanyar keta kundin tsarin mulki da doka.

Ana kuma zargin Trump da tattaro zugar da suka aikata zanga-zangar mai cike da aika-aika a birnin Washington, tare da jagorantar su zuwa Capitol duk da sanin cewa suna dauke da manyan bindigogi, da sauran makamai masu yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.