Isa ga babban shafi

Za mu lalata makamai masu linzami da Amurka za ta tura Ukraine - Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce yana da kwarin guiwa dari bisa dari cewa dakarunsa za su ruguza tsarin tsaron sararin sama na Pentagon da shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin turawa Ukraine.

Shugaban Rasha Vladmir Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Tabbas za mu lalata duk wani makami mai linzami," in ji Putin ya ce, yayin da yake magana kan wani makami mai linzami na Patriot da Amurka ta yi alkawarin ba wa Ukraine.

Shugaba Vladimir ya caccaki kasashen yammacin duniya da ke kokarin raba kasar Rasha.

Babban abin da ke gabanmu shi ne manufofin abokan adawar mu na yammaci, da nufin wargaza kasarmu Rasha mai cike da tarihi, "in ji Putin.

"A koyaushe suna kokari su sanya mana rarrabuwar kawuna, kuma burinmu wani abu ne dabam don mu yi nasara wajen hada kan al'ummar Rasha."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.