Isa ga babban shafi

Fafaroma Benedict ya mutu ya na da shekaru 95 a Duniya

Tsohon shugaban darikar Katlika na Duniya Fafaroma Benedict ya mutu yau asabar yana da shekaru 95 a Duniya, kusan shekaru 10 bayan matakinsa na murabus daga jagorancin darikar irinsa na farko da aka taba samu cikin karni 6 da suka gabata.

Fafaroma Benedict, dan kasar Jamus da ya yi murabus daga jagorancin darikar Katlika shekaru 10 da suka gabata.
Fafaroma Benedict, dan kasar Jamus da ya yi murabus daga jagorancin darikar Katlika shekaru 10 da suka gabata. © vaticannews.va
Talla

Fadar Vertican ta sanar da mutuwar tsohon babban limamin na ta wanda ya yi fama da jinya tsawon lokaci.

Cikin sanarwar da fadar ta Vetican ta fitar ta ce Benedict ya mutu a safiyar yau asabar da misalin karfe 9 da mintuna 34 a dakin bauta na Mater Ecclesiae Monastery da ke cikin fadar ta Vatican.

Kakakin fadar ta Vatican Matteo Bruni ya ce tsohon babban limamin dan kasar Jamus ya cika cikin salama a dakin bautar bayan fama da rashin lafiyar tsawon lokaci, ko da ya ke bai sanar da lokacin jana’iza ba.

Fafaroma Benedict wanda ainahin sunansa shi ne Joseph Ratzinger ya ci gaba da rayuwa a cikin fadar ta Vatican ne duk da matakinsa na murabus a watan Fabarairun shekarar 2013.

Benedict ya yi ta fama da rashin lafiya, sai dai a larabar da ta gabata ne fadar ta Vatican ta fitar da sanarwar cewa jikinsa ya matsananta yayinda Fafaroma Francis ya bukaci Duniya ta yi masa addu’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.