Isa ga babban shafi

Kevin McCarthy ya zama sabon kakakin Majalisar wakilan Amurka

Kevin McCarthy na jam’iyyyar Repulican ya zama sabon kakakin majalisar wakilan Amurka, bayan da aka shafe tsawon kwanaki ana fafatawa wajen kada kuri'a tsakanin magoya bayansa, da masu adawa da shi.

An rantsar da sabon kakakin majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy
An rantsar da sabon kakakin majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy © REUTERS / EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Sai da aka gudanar da zaben kujerar kakakin majalisar wakilan ta Amurka sau 15, kafin McCarthy ya samu nasarar da kuri’u 216, yayin da abokin hamayyarsa Hakeem Jeffries ya samu kuri’u 212 a zagayen karshe na zaben da aka yi a daren Juma’ar da ta gabata.

Wannan dai shi ne karo na farko a cikin shekaru 160 da aka gaza zaben sabon kakakin majalisar a zagayen farko na zaben da aka saba yi.

Da kyar ne dai 'yan jam'iyyar Republican suka samu nasarar yin rinjaye a majalisar dokokin Amurkan, bayan zaben tsakiyar wa'adi da aka gudanar a watan Nuwamba, inda su kuma 'yan Democrat suka karbe jagorancin majalisar dattawan kasar.

Tuni dai aka rantsar da sabon kakakin majalisar wakilan na Amurka Kevin McCarthy da safiyar yau asabar bayan gwagwarmayar ta tsawon kwanaki.

Fafatawa mafi dadewa tsakanin ‘yan takarar zama kakakin majalisar wakilan Amurka ita ce wadda aka gani a shekara ta 1855.

A waccan lokacin dai sai da aka shafe sama da watanni biyu kafin a karkare zaben, wanda  muhawara kan bayi da kuma yakin basasa ya mamaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.