Isa ga babban shafi

Amurka na shirin tsaurara dokokin shigarta ga 'yan China saboda Korona

Gwamnatin Amurka na duba yiwuwar fara tsaurara matakan dakile annobar COVID-19 kan matafiyan da ke shiga kasar daga China, saboda rashin gamsuwa da bayanan da ke fitowa daga kasar ta Sin a game da adadin mutane da ke kamuwa da cutar a yanzu haka.

'Yan kasar China sanye da takunkumin rufe hanci da baki a tashar jiragen kasa dake karkashin kasa a garin Shanghai.
'Yan kasar China sanye da takunkumin rufe hanci da baki a tashar jiragen kasa dake karkashin kasa a garin Shanghai. REUTERS - ALY SONG
Talla

Matakin na Amurka ya zo ne bayan da Japan, India da Malaysia suka sanar da daukar tsauraran matakai kan matafiya daga China a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, saboda karuwar wadanda ke kamuwa da cutar a kasar.

Kasar Japan ta ce za ta bukaci gwajin COVID-19 ga dukkanin baki daga China da zarar sun sauka a kasar.

Gwamnatocin kasashe da dama dai na cigaba da bayyana damuwa game da karuwar masu kamuwa dda cutar COVID-19 a kasar Sin, da kuma rashin samun gamsassun bayanai da suke  samu daga mahukuntan kasar.

Asibitoci da dama a kasar Sin yanzu haka sun cika makil da marasa lafiya sakamakon sake bazuwa da Korona ke yi a sassan kasar mai mutane biliyan 1 da miliyan 400.

Sai dai duk da haka alkaluman hukuma sun nuna cewar mutum guda ne kawai cutar ta kashe a cikin kwanaki bakwai zuwa ranar Litinin, lamarin da ya haifar da shakku tsakanin masana kiwon lafiya game da bayanan na  gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.