Idan aka kaiwa Belarus farmaki za mu bi sahun Rasha - Lukashenko
Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus y ace kasar a shirye take ta yi yaki tare da babbar kawarta Rasha a Ukraine idan aka kai wa kasarsa hari.
Wallafawa ranar:
"A shirye nake da na marawa Rasha baya daga Belarus ba tare da bata lokaci ba: Idan ko da soja daya ya zo cikin yankin Belarus don ya kashe mutanena," shakka babu zan hada kai da Rasha wajen daukar fansa,” in ji Lukashenko a wani taron manema labarai.
Ya kara da cewa "Idan suka yi ta'addanci a kan Belarus, martani zai kasance mafi tsanani, kuma yakin zai dauki salo daban-daban."
Sojojin Rasha sun yi amfani da yankin Belarus a matsayin wurin kaddamar da farmakin da aka kai wa Ukraine a watan Fabrairun da ya gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu