Isa ga babban shafi

Rasha na yaki ne a Ukraine domin kwato yankunan ta na tarihi - Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin yace kasar na yaki ne a kasar Ukraine domin kwato yankunanta na tarihi yayin gudanar da wani gagarumin biki a birnin Moscow domin goyan bayan yakin da kasar ta kaddamar. 

Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan
Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan RFI
Talla

Putin ya shaidawa gangamin taron jama’ar cewar ya jiyo daga manyan kwamandodin sojin kasar cewar yanzu haka ana ci gaba da musayar wuta domin ceto jama’arsu da kuma yankunansu na tarihi. 

Yayin gabatar da wani takaitaccen jawabi ga taron wanda ya samu halartar dubun dubatan mutane a filin wasan Luzhiniki, Putin ya jinjinawa sojojin kasar dake sadaukar da rayukansu a Ukraine inda yace suna alfahari da su. 

Shugaban kasar yace duk wadanda suka goyi bayan yakin da sojojin kasar suke yi, kamar suma sun je fagen daga ne domin kare kasarsu. 

Putin ya bayyana ma’aikatan kula da lafiya da ma’aikatan dake aiki a ma’aikatar tsaro da sufuri da ma sauran jama’ar kasar a matsayin masu bada gudumawa saboda goyan bayan yakin. 

Wadanda suka halarci gangamin suna dauke da tutar Rasha inda suka bijirewa sanyin da ake yi a kasar wanda ke kasa da maki 15 domin nuna goyan bayansu ga kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.