Isa ga babban shafi

An cika shekara guda da barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine

Yau ake cika shekara guda cif da faro yakin Rasha a Ukraine, inda zuwa yanzu Moscow ta kwace iko da yankuna da dama wanda ya kai ga asarar dubunnan sojoji daga bangarorin biyu dai dai lokacin da Shugaba Volodymyr Zelensky ke shan alwashin samun nasara a yakin, a bangare guda kuma Rasha ke ci gaba da ganin takunkuman karya tattalin arziki daga kasashen yammacin Duniya.

Dubunnan sojoji suka kwanta dama daga dukkanin bangarorin biyu.
Dubunnan sojoji suka kwanta dama daga dukkanin bangarorin biyu. AP - Leo Correa
Talla

Wannan yaki da ya yi sanadiyyar rasa dimbin rayuka, ya nuna yadda shugabannin kasashen yammacin duniya ke marawa Ukraine baya tare da kakabawa Rasha takunkumi, ciki har da wasu sabbi da ministocin kungiyar kasashen G7 suka amince da su. 

Zelensky ya ce za su ci gaba da sadaukar da rayukansu wajen yakin, domin har yanzu gwiwar su bata yi sanyi ba, ganin yadda suka yi ta tsallake shingen da abokan gaba ke kafa musu. 

Shugaban kasar ya ce za su ci gaba da gabatar da bukatar ganin an hukunta duk wanda ya taimaka wajen kai yakin cikin kasar su da kuma jefa ta cikin mawuyacin hali. 

Mazauna birnin Kiev wanda sojojin Rasha suka yi kokarin mamayewa a watan fabarairun bara na ci gaba da bayyana jajircewar su duk da irin dimbin ta’adin da aka musu wajen lalata gine gine da kuma kayan more rayuwa. 

Diana Shestakova mai shekaru 23 tace tana da yakinin zasu samu nasarar yakin, sai dai basu san lokacin da za a iya kammala shi ba. 

Rahotanni sun ce akalla kowanne bangare yayi asarar sojojin da suka kai 150,000. 

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce suna yakin ne domin kwato yankunan kasar su na tarihi dake Ukraine, yayin da shugaban Amurka Joe Biden ke cewa Rasha ta tafka babban kuskure wajen kai mamayar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.