Isa ga babban shafi

China ta bukaci Rasha da Ukraine su gaggauta fara zaman sulhu

China ta bukaci Ukraine da Rasha su gaggauta gudanar da zaman tattaunawar sulhu domin kawo karshen tashin tashina dake tsakanin Kasashen biyu, inda Ukraine ke cewa kiran ya tabo batun samawa iyakokinta martabarsu.

Ministan harkokin wajen China, Qin Gang.
Ministan harkokin wajen China, Qin Gang. AP - Andy Wong
Talla

Yayin zantawarsu ta wayar tarho Ministan harkokin wajen China Qin Gang ya fada wa takwararsa na Ukraine Dmytro Kuleba cewa, China na sa ran bangarorin biyu su yi hakuri da juna, su kuma mayar da wukan su kube, tare da amincewa da gudanar da zaman tattaunawar sulhu.

Kazalika Qin ya ce matsayar China daya ce game da rikicin Rasha da Ukraine, wato goyon bayan kudurin gudanar da tattaunawar sulhu wanda ake sa ran ya zama silar kawo karshen yakin da aka shafe sama da shekarar daya ana gwabzawa.

Wannan ne karon farko da China ke yin kira a hukumance tun bayan ministan harkokin wajen Kasar ya soma aiki a cikin watan disamban shekarar shekarar bara.

Kasashen yammacin duniya sun caccaki China a kan rashin caccakar Rasha na yin mamaya a Ukraine, wanda ko a cikin watan da ya gabata Chinan ta musanta zargin da Amurka ta yi mata na yunkurin taimakawa Rasha da makaman yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.