China ta goyi bayan Rasha kan matakinta na kin janyewa daga yakin Ukraine
China ta marawa Rasha baya kan kudirinta na kin janyewa daga yakin da ta ke yi a Ukraine kamar yadda wata sanarwar taron ministocin kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki na G20 da ke gudana a birnin New Delhi na india ta sanar.
Wallafawa ranar:
China da Rasha, su kadai ne daga cikin mambobin kasashen G20 suka ki amincewa da sanarwar da ke bukatar Rasha da ta janye baki daya kuma nan take daga kasar Ukraine.
Ministan Harkokin Wajen China, Qin Gang ya ce, za su ci gaba da zantawa da Rasha da kuma ba ta hadin-kai a dukkanin matakai a yayin taron na G20.
Ko da ya ke Mista Gang ya ce, ya shaida wa takwaransa na Rasha Sergey Lavrov cewa, suna goyon bayan Moscow dari bisa dari kan shiga tattaunawar zaman lafiya kuma Chinar a shirye ta ke ta taka rawa a wannan fannin a cewarsa.
Akasarin mambobin kasashen G20 sun yi tir da yakin da ake yi a Ukraine, in ban da Rasha da China da suka nuna ko-oho.
Kasashen yammaci dai na cike da fargaba kan yiwuwar Chinan ta fara taimakawa Rasha da makamai, batun da ke cikin abubuwan da za a tattauna a taron na G20.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu