Isa ga babban shafi

Algeria da Rasha na shirin karfafa aikin hadin gwiwa na soji

Ma'aikatar tsaron Algeria ta bayyana cewa, kasar da Rasha sun tattauna kan karfafa hadin gwiwarsu na soji, a ziyarar da sakataren kwamitin tsaron kasar Rasha Nicholai Patrushev ya kai birnin Algiers.

Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune tare da shugaban Rasha Vladmir Putin
Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune tare da shugaban Rasha Vladmir Putin © TFIGlobal
Talla

Jami'in na Rasha tare da rakiyar wata babbar tawaga, sun tattauna da babban hafsan hafsoshin sojin kasar Algeria, Said Chanegriha, kan yanayin aikin hadin gwiwar soji tsakanin kasashen biyu da kuma hanyoyin karfafa shi," a cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar.

Wannan ziyarar tana wakiltar, tsayin daka da amincewar kasashen biyu don kara karfafa dangantaka bisa manyan tsare-tsare da tarihi, musamman a fannin hadin gwiwar soji," in ji Chanegriha.

Patrushev, wanda aka nakalto a cikin sanarwar, ya ce a nasa bangaren kasarsa na kokarin kara karfafa alaka tsakanin Algeria da Rasha.

A yayin wannan ziyarar, shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya tarbi sakataren kwamitin tsaron kasar ta Rasha, kamar yadda wasu hotuna da gidan talabijin din kasar suka nuna.

Moscow dai ita ce babbar mai samar da makamai ga Algeria, kasa mafi girma a Afirka.

Rahotanni daga kasar na cewa, Tebboune zai kai ziyarar aiki kasar Rasha a watan Mayu.

Algiers da Moscow suna da wata dadaddiyar alakar a fannoni da dama.

A cikin shekarar 2021, cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai dala biliyan uku, kuma, duk da barkewar annobar Covid-19, an samu ci gaba sosai ta fannin cinikayya a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.