Isa ga babban shafi

Kotu ta dage shari'ar Trump zuwa 2024 bayan ya musanta zarge-zarge 34

Kotu a birnin New York ta saki Donald Trump ba tare gindaya wasu sharudda ba a shari’ar da aka faro kan tsohon shugaban na Amurka dangane da zarge-zarge masu alaka da biyan makuden kudade gabanin zaben shekarar 2016.

Donald Trump shugaba na farko daga Amurka tsoho ko mai ci da ya taba gurfana gaban kotu.
Donald Trump shugaba na farko daga Amurka tsoho ko mai ci da ya taba gurfana gaban kotu. REUTERS - JONATHAN ERNST
Talla

Trump wanda ya musanta dukkanin tuhume-tuhume 34 da ake kansa, yayin zaman shari’ar na jiya karkashin jagorancin mai shari’a Juan Merchan wanda ke matsayin karon farko a tarihin Amurka da wani shugaba tsoho ko mai ci ya taba gurfana gaban kotu, ya bayyana shari'ar da makarkashiya gare shi.

Alkalin da ya jagoranci shari’ar Juan Merchan ya dage lokacin ci gaba da sauraron shari’ar zuwa watan Janairun shekarar 2024, ko da ya ke lauyoyin Trump sun bukaci dawo da lokacin kurkusa, lura da yadda lokacin shari’ar ya yi dai dai da lokacin zaben fidda gwani don tunkarar zaben shugaban kasa na shekarar, zaben da Trump ke shirin sake tsayawa takara.

Cikin tuhume-tuhume 34 da ake kan Trump dai har da biyan makuden kudade ga mabanbantan mutane wadanda ake ganin su suka kai shi ga nasara a zaben na 2016, ciki har da jarumar fina-fina batsa da ya yi mu’amala da ita da kuma wani da ke da bayanin yadda tsohon shugaban ke da wani da da ya Haifa ba tare da aure ba.

Sauran tuhume-tuhumen da Trump ya musanta akwai tayar da hankali tare da tunzura magoya bayansa bayan faduwa a zaben 2019 wanda ya kai ga rikicin Capitol da ya yi sanadin mutuwar mutane 6.

Sai dai a jawabinsa gaban dubban magoya bayansa a wata fadarsa da ke bakin ruwa a birnin Florida, Trump mai shekaru 76 ya bayyana tuhumar a matsayin cin mutunci ga Amurka baki daya, ya na mai cewa laifi daya da ya san ya aikata ba tare da tsoro ba shi ne bayar da kariya ga Amurka daga masu yunkurin rusa ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.