Isa ga babban shafi

Shugaban Faransa ya kammala ziyarar kwanaki uku a kasar China

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya samu tarba daga dimbin jama'a a wata jami'a da ke kudancin kasar China a ranar Juma'a, daidai lokacin da yake dab da kammala ziyarar kwanaki uku da ya kai kasar, inda ya sha matsawa takwaransa Xi Jinping ya taimaka wajen kawo karshen rikicin Ukraine.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron lokacin da ya gabatar da jawabi a jami'ar Sun Yat-Sen da ke Guangzhou, a kasar China, ranar Juma'a, 7 ga Afrilu, 2023.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron lokacin da ya gabatar da jawabi a jami'ar Sun Yat-Sen da ke Guangzhou, a kasar China, ranar Juma'a, 7 ga Afrilu, 2023. AP - Thibault Camus
Talla

Macron wanda ya sauka a birnin Beijing babban birnin kasar a ranar Laraba, ya ce yana neman China da ta shiga rikicin da ke wakana tsakanin Rasha da Ukraine.

A ranar Juma'a, shugaban na Faransa ya tashi zuwa birnin Guangzhou da ke kudancin kasar, inda daruruwan dalibai ke neman daukar hoton selfie tare da Macron din.

Macron, wanda wasu daga cikin daliban suka yi ta rera sunansa, ya gana da su a dakin motsa jiki na jami'ar, ya kuma amsa tambayoyinsu kafin liyafar cin abincin dare da Xi, gabanin ganawa da masu zuba jari na kasar China, yayin da ya kammala ziyarar kwanaki uku a kasar.

Rikicin Rasha da Ukraine ya mamaye ziyarar da Macron ya kai China na farko tun shekarar 2019.

Shugaban na Faransa, ya kuma shaidawa daliban a Guangzhou cewa yakin da ke wakana a Ukraine, shakka babu ya ci karo da dokokin kasa-da-kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.