Isa ga babban shafi

Kotu a Faransa ta amince da sabuwar dokar fansho

Kotun tsarin mulki ta Faransa ta amince da sabon shirin fansho da Emmanuel Macron ke shirin tabbatarwa a tsakanin ma’aikatan kasar, wanda ya haifar da cece-kuce da kuma jerin zanga-zanga. 

Yadda masu zanga-zanga suka fito maci a biranen Faransa, kan adawa da sabuwar dokar fansho.
Yadda masu zanga-zanga suka fito maci a biranen Faransa, kan adawa da sabuwar dokar fansho. REUTERS - STEPHANE MAHE
Talla

Wannan amincewa dai zata ba wa Macron damar tabbatar da dokar a tsakanin ma’aikatan kasar. 

Kotun mai mambobin mutum 9 ta amince da sabuwar dokar fanshon wadda ta hadar da karin shekarun ritaya daga 62 zuwa shekaru 64, abinda ke nufin yanzu ya zama doka. 

Sai dai kuma kotun ta yi watsi da wasu bukatu guda 6 da gwamnatin Macron din ta ke son a tabbatar da su, cikin su har da tilastawa manyan kamfanoni fitar da bayanan ma’aikatan su ‘yan kasa da shekaru 55. 

Wannan dai na nufin Macron ya samu nasara a kan miliyoyin al’ummar kasar da suka rika nuna kyama kan wannan sabuwar doka, wadda suke ganin take hakki ne a gare su, yayin da suka shafe tsawon watanni uku suna gudanar da zanga-zangar adawa da ita. 

Bayanai sun bayyana cewa a yayin zaman kotun na ranar Juma'a, ‘yan sanda sama da dubu 10 ne suka yiwa kotun kawanya don kare faruwar zanga-zanga zuwa cikin kotun ko kuma arangama tsakanin jama’a da alkalai. 

Sai dai kuma faifan bidiyo da suka fita sun nuna yadda dubban mutane da ke wajen kotun suka rika yiwa alkalai ihu da tofin alatsine, bayan da suka fito daga kotun jim kadan bayan yanke hukuncin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.