Isa ga babban shafi

Zanga-Zangar dokar Fansho a Faransa ta haifar da tsaiko ga sufuri da makarantu

Ayyukan sufurin jiragen kasa da Jiragen kasa masu aiki a kwaryar birnin Paris na kasar Faransa da Makarantu kazalika da filayen jirage na shirin dakatar da baki dayan aikinsu sakamakon zanga-zangar da ma’aikata ke yi kan sauyin shekarun ajiye aiki a kasar ta Faransa. Ana kuma sa ran dakile ayyukan makarantu ma a kasar ta Faransa sakamakon zanga-zangar da akalla mutane dubu 757 suka fito.  

Masu zanga-zangar adawa da dokar fansho a Faransa.
Masu zanga-zangar adawa da dokar fansho a Faransa. AP - Michel Euler
Talla

Duk da cewar Zanga-Zangar ta taba baki dayan harkokin sufuri a kasar Faransa, kamfanin sufurin Jiragen kasa ya ce har yanzu Jirage masu tafiyar nisan zango na aiki amma a rabin zangon da ya saba. 

Yanzu haka dai an ce a kowanne ma’aikata biyu na kamfanin tace danyen Mai a ma’aikatar Mai ta TotalEnergies sun daina zuwa aiki, kamar yadda kamfanin ya bayyana, amma Man da aka adana a gidajen Mai ka iya magance dan tsaikon da za’a samu na shayar da masu ababen hawa a gidajen Mai. 

To sai dai bukatar da shugaban kasar Faransa Emannuel Macron ya gabatar na kusa da tanadin makwabtan kasashen Turai da akasarinsu ke da shekaru 65 ne na ajiye aiki. 

Kuma gwamnatin kasar na kokarin fahimtar da mutane akan cewar akwai dan adalci a tsarin fanshon da ta dauko, da ta ce ya yi daidai kuma ma, masana harkokin tattalin arzikin kasar na cewar wajibi ne ma’aikata da ba su da isasshiyar kwarewa su hakura da abinda gwamnati ta shata. 

Amma a yanda Ministan kula da ra’ayoyin jama’a na kasar Gabriel Attal ya shaida wa Majalisar kasar ranar Litinin da ta gabata, abinda gwamnatin ke son yi ba sauyi ba ne, tabarbarar da tsarin ne da kuma ya haifar da soke-soke daga ‘yan hamayya.     

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.