Isa ga babban shafi

An ga jinjirin watan Shawwal a Najeriya

Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na uku, ya sanar da cewa za a gudanar da Idin karamar Sallah, ranar 21 ga watan Afrilun 2023, daidai da 01 ga watan Shawwal 1444 Hijiriyya.

Sarkin Sokoto, Abubakar Sa'ad
Sarkin Sokoto, Abubakar Sa'ad © ©ifm923
Talla

Maigirma Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, wanda shine shugaban kwamitin tantance ganin watan, ya tabbatar da ganin watan.

Sanarwar ta ruwaito Sarkin Musulmi na cewa, mambobin kwamitin sun samu rahotanni daga wurare daban-daban a sassan Najeriya, inda suka zauna da masana domin tabbatar da ingancin ganin watan na bana.

Najeriya dai ta kasance daga cikin kasashen da za su gudanar da Idin karamar Sallah a ranar Juma'a, yayin da wasu kasashen kuma za su fara gudanar da nasu bukukuwan Sallar daga ranar Asabar, 22 ga watan Afrilun 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.