Isa ga babban shafi

Amurka ta zargi Afirka ta Kudu da baiwa Rasha makamai domin mamaye Ukraine

Kasar Amurka ta zargi Afirka ta Kudu da taimakawa Rasha da makamai domin anfani da su wajen mamayar kasar Ukraine, duk da ta bayyana matsayin ta na ‘yar ba ruwan mu a cikin wannan rikicin. 

Shugaban Amurka Joe Biden yayin jawabi a fadar White House. 1/05/23
Shugaban Amurka Joe Biden yayin jawabi a fadar White House. 1/05/23 AP - Susan Walsh
Talla

Jakadan Amurka a Johanesburg Ambasada Reuben Brigety ya bayyana cewar a watan Disambar shekarar da ta gabata, an ga lokacin da Afirka ta Kudu tayi lodin makamai a gabar jirgin ruwan Cape Town domin aikewa da su zuwa Rasha. 

Jakadan yace baiwa Rasha makamai matsala ce mai girma wadda basa tunanin ana iya warware ta, yayin da suke bukatar Afirka ta Kudu da ta ci gaba da rike matsayin ta na ‘yar ba ruwan mu. 

Kasar Afirka ta kudu taki fitowa fili ta soki matakin da Rasha ta dauka na mamaye Ukraine wanda ya haifar da takun saka tsakanin kasashen yammacin duniya da gwamnatin Vladimir Putin. 

Ita dai Afirka ta kudu mai karfin fada aji a siyasar duniya taki hada kai da sauran kasashen duniya wajen Allah wadai da yakin, inda ta bukaci tattaunawa domin kawo karshen rikicin. 

Sai dai a farkon wannan shekarar sojojin ta sun yi wani atisayen hadin gwuiwa tsakaninsu da sojojin Rasha da kuma China, abinda ke nuna inda bakin ta ya karkata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.