Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu - Amurka

Ramaphosa da Biden sun tattauna kan rikicin Rasha da Ukraine

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Amurka Joe Biden, kwana guda bayan da kasar ta kauracewa kada kuri'a kan kudirin dakatar da kasar Rasha daga hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya kan cin zarafin da ta yi a Ukraine.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa © AFP
Talla

Ramaphosa, wanda ake sukar gwamnatinsa da kin yin Allah wadai kan mamayar da Rasha ta yi a Ukraine, ya caccaki kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a zamanantar da shi.

Sa'o'i kadan bayan haka, Afirka ta Kudu na daga cikin kasashe 58 da suka ki kada kuri'a kan kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya dakatar da Rasha daga kwamitin kare hakkin bil'adama na MDD a matsayin ladabtar da mamayar Ukraine.

Wannan dai shi ne karo na uku da Afirka ta Kudu ke kauracewa kada kuri'a kan kudurorin da aka amince da su kan yakin.

Ramaphosa ya wallafa a shafinsa na twitter a wannan  Juma'a cewa ya tattauna da shugaba Biden ta wayar tarho, kuma sun amince amince da bukatar tsagaita bude wuta da tattaunawa tsakanin Ukraine da Rasha."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.