Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu-Rasha-Ukraine

Ramaphosa ya zargi NATO da hannu a rikicin Rasha da Ukraine

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya zargi kungiyar tsaro ta NATO da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, sai dai ya  ce ba zai yi watsi da kiran da ake yi na yin Allah wadai da Rasha ba, a cikin kalaman da ke nuna shakku kan ko Ukraine ko kasashen Yamma za su amince da shi a matsayin mai shiga tsakani.

Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa.
Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa. © AP/Nic Bothma
Talla

Ramaphosa, wanda ke Magana a gaban majalisar dokokin kasar, ya ce da NATO ta yi biyayya ga gargadin da aka yiwa shugabanninta tsawon shekaru da suka wuce, musamman yadda take yunkurin fadadawa zuwa yankin gabashin Turai da yanzu wannan yaki bai auku ba.

Shugaba Vladimir Putin ya kwatanta ayyukan Rasha a matsayin aiki na musamman don karya ikon karfin wasu sojoji da kuma kawo karshen akidar ‘yan nazi a Ukraine tare da magance abin da ya kira zaluncin NATO.

Ramaphosa ya kuma bayyana cewa, Putin ya tabbatar masa da kansa cewa tattaunawar na samun ci gaba, amma ya ce har yanzu bai tattauna da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ba sai dai nan gaba.

Shugaban dai ya ce an bukaci Afirka ta Kudu da ta shiga tsakani a rikicin Rasha da Ukraine, sai dai bai bayyana wanda ya nemi ya sa baki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.