Isa ga babban shafi

Syria na halartar taron kasashen Larabawa karon farko cikin shekaru 11

A karon farko cikin shekaru 11 Syria ta samu sukunin haskawa a taron kasashen larabawa bayan aike mata da goron gayyata a yau litinin, gabanin babban taron kungiyar da za a bude ranar juma’a mai zuwa a Saudi Arabia.

Taron kasashen Larabawa a Saudi Arabia.
Taron kasashen Larabawa a Saudi Arabia. © AMR ABDALLAH DALSH / REUTERS
Talla

A wani jawabi da ya gabatar ta gidan talabijin, ministan kudin Saudi Arabia Mohammed al-Jadaan ya ce a shirye kasar ta ke ta karbi bakoncin Syria a taron.

Cikin jawabin nasa a dai dai lokacin da kyamara ta haska fuskar wakilin Syria ta tuni ya isa Saudiya, Jadaan ya ce kofa a bude ta ke wajen ganin an yi aiki tare tsakanin dukkanin kasashen yankin don samun nasara kan kudire-kudiren da suka sanya a gaba.

Wannan ne dai karon farko da wani wakili daga Syria ke halartar taron kungiyar ta kasashen larabawa tun bayan dakatarwar da kasar ta fuskanta a shekarar 2011.

Alaka ta yi tsami tsakanin gwamnatin Syria da kungiyar kasashen larabawa ne tun bayan zanga-zangar kasar da ta juye zuwa rikici tare da haddasa asarar rayukan mutanen da yawansu ya haura dubu dari 500 a shekaru 12 da suka gabata.

Sai dai bayan kakkarfar girgizar kasar da Syrian ta fuskanta a farkon shekarar nan da kuma yadda kasashen larabawan suka rika tururuwar taimaka mata, dama an yi tsammanin dawowar alakar.

A farkon watan nan ne dai, Kungiyar kasashen larabawan ta dawo da Syria cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.