Isa ga babban shafi

Taron kasashen Larabawa zai tattauna batun Sudan da Syria

Jami’an diflomasiyya daga kasashen Larabawa na shirin wani taron gaggawa a birnin Alkahira na kasar Masar a a ranar Lahadi don tattauna batun yakin da ake a Sudan da kuma yiwuwar maido da kasar Syria cikin kungiyar, sama da shekaru 10 bayan dakatar da ita.

Ministocin harkokin kasashen waje za su hallara a birnin Alkahira na kasar  Masar.
Ministocin harkokin kasashen waje za su hallara a birnin Alkahira na kasar Masar. AP - Anis Belghoul
Talla

Taron na Lahadi, in ji kakakin kungiyar, Gamal Rushdy, na zuwa ne bayan da wasu kasashen Larabawa suka maaido da dangantaka tsakaninsu da shugaban Syria, Bashar al-Assad, kuma ministocin harkokin wajensu suka ziyarci birnin Damascus a makwannin da suka gabata.

Shi ma ministan harkokin wajen Syria ya ziyarci birnin Alkahira da Riyadh na Saudiyya a karon farko cikin shekaru sama da 10.

Saudiyya ce za ta karbi bakuncin taron na ranar 19 ga watan Mayun nan, kuma ana sa ran a tattauna  batun maido da Syria cikin kungiyar.

Sai dai wasu daga cikin mambobin kungiyar, musamman Qatar ba ta goyon bayan maido da Syria cikin kungiyar kasashen Larabawa.

A watan Nuwamban shekarar 2011 ne 18 daga cikin mambobin kungiyar 22 suka amince da dakatar da Syria daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.