Isa ga babban shafi

Kungiyar G7 na duba yuwuwar yadda za a tsaurarawa Rasha takunkumi

Shugabannin kungiyar G7 sun isa birnin Hiroshima na kasar Japan, domin tattaunawa kan yadda za a tsauraran takunkumin da aka kakabawa kasar Rasha, da hakan masana ke ganin zai kasance barazana ga tattalin arzikin kasar China.

Kasashen Turai na duba yuwuwar yadda za a kassara tattalin arzzikin Rasha
Kasashen Turai na duba yuwuwar yadda za a kassara tattalin arzzikin Rasha © AP/Susan Walsh
Talla

Firaministan Japan Fumio Kishida na karbar bakuncin shugabannin daga wasu kasashe shida masu karfin tattalin arziki, a guda daga cikin biranen kasar da ya taba fuskantar harin makaman nukiliya, kuma a yanzu cike yake da abubuwan tunawa.

Shugabanni da suka hada da shugaban Amurka Joe Biden za su yi kokari na tsawon kwanaki uku don samar da hadin kai a kan Rasha da China, inda sau dama maslahar kawance kasashen ba sa samar da mafita.

Shirin warware rikicin diflomasiyya da ya dabaibaye shugaba Biden a yankin Asiya ya ci karo da cikas tun kafin ya bar kasar Amurka, sakamakon takaddamar kasafin kudi na cikin gida da ya tilasta masa soke tsayawa a Papua New Guinea da Australia.

Yunkurin mamayar da Rasha ta yi na watanni 15 a Ukraine, shi ne kan gaba wajen tattaunawa a kai a taron kolin G7 a ranar Juma'a, bayan wani sabon hari ta sama da aka kai a Kyiv da kuma Bakhmut da sauran garuruwan Ukraine.

Amurka da kawayenta sun tura makami zuwa Ukraine domin dakile ci gaban da Rasha ta samu, amma har yanzu ba a kai ga dakatar da kai hare-hare da sojojin Kyiv suka dade suna fafutuka a kai ba.

Ana sa ran shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky zai yi jawabi ga shugabannin kungiyar ta yanar gizo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.