Isa ga babban shafi

Taron minstocin harkokin wajen G7 zai mayar da hankali kan Asiya da Ukraine

Ministocin harkokin waje na kasashen G7 sun sauka a birnin Karuizawa na Japan a yau Lahadi domin ganawa mai mahimmanci, wadda batun matsin lambar China a kan Taiwan da yakin Ukraine da Rasha zai mamaye.

Taron zai matyar da hankali a kan matsalolin nahiyar Asiya da yakin Ukraine.
Taron zai matyar da hankali a kan matsalolin nahiyar Asiya da yakin Ukraine. © Aleph news
Talla

Akwai batutuwa da dama da suka shafi diflomasiyya da tsaro, wadanda za a tattauna, amma za a fi mayar da hankali ne  a kan yankin nahiyar Asiya.

Wannan taro na zuwa ne kwanaki bayan da China ta kammala wani gagarumn atisayen soji a kewayen Taiwan mai kwarya-kwaryar cin gashin kai, inda kuma ta hana jiragen ruwa zuwa wani yanki na arewacin tsibirin.

A ranar Alhamis, Koriya ta Arewa kaddamar da wani sabon makami mai linzami mai cin dogon zango, gwaji na baya bayan nan daga cikin jerin gwaje gwajen da suka tayar da hankali a nahiyar.

A matsayinta na mai daukar nauyin taron wannan shekarar, Japan ta kagara ta tabbatar da cewa kalubalen da nahiyar Asiya ke fuskanta ne suka kasance mahimman batutuwan da za a tattauna, kana za ta yi Karin haske a kan ammanar da ta yi cewa mamayar Ukraine da Rasha ta yi ta jaddada bukatar yin taka tsantsan a  nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.