Isa ga babban shafi

G7 ta sha alwashin ci gaba da marawa Ukraine baya

Shugabannin kasashe bakwai masu karfin tattalin ararzikin masana'antu a duniya G7,  sun lashi takobin ci gaba da marawa Ukraine baya dangane da mamayar da Rasha ta yi mata.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya halarci taron shugabannin G7 ta sadarwar bidiyo, yayin da Rasha ke ci gaba da kai hari a Ukraine,  27, ga watan Yuni 2022.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya halarci taron shugabannin G7 ta sadarwar bidiyo, yayin da Rasha ke ci gaba da kai hari a Ukraine, 27, ga watan Yuni 2022. VIA REUTERS - UKRAINIAN PRESIDENTIAL PRESS SER
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar yayin taronta a kudancin Jamus, kungiyar G7 tace, "Za ta ci gaba da baiwa kasar Ukraine tallafin kudi da na jin kai har da na soji da kuma na diflomasiyya tare da tsayawa kafa-da-kada da kasar da yaki ya dai-daita.

Shugabannin kasashe bakwai masu karfin tattalin ararzikin masana'antu a duniya G7,  sun lashi takobin ci gaba da marawa Ukraine baya dangane da mamayar da Rasha ta yi mata.
Shugabannin kasashe bakwai masu karfin tattalin ararzikin masana'antu a duniya G7, sun lashi takobin ci gaba da marawa Ukraine baya dangane da mamayar da Rasha ta yi mata. REUTERS - POOL

Wannan sakon marawa Ukraine baya na fitowa ne bayan tattaunawar sama da sa’o’i biyu da shugabannin gungun G7 suka yi da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ta hoton bidiyo.

Harin makami mai linzami Kiev

Shugaban gwamnatin Jamus mai masaukin baki Olaf Scholz ta shafinsa na twitter ya wallafa goyan bayan kungiyar na tsayawa kai da fata don taimakawa Ukraine da tuni babban birninta Kiev ya fuskanci farmaki makami mai linzami daga Rasha.

Scholz na mai cewa dole su dauki matakai masu tsauri da kuma suka dace, tare da kara matsin lamba kan Putin, don kawo karshen yakin.

Karancin abinci

Mambobin kungiyar sun gargadi Rasha kan bada damar jigilar kayayyakin abinci ficewa daga Ukraine domin kaucewa ta'azzara matsalar karancin abinci a duniya.

"Muna kira ga Rasha cikin gaggawa da ta daina kai hare-hare kan ayyukan noma da sufuri, ba tare da wani sharadi ba, tare da ba da damar jigilar kayan amfanin gona kyauta daga tashar jiragen ruwa na Ukraine dake tekun Black Sea," 

Shugabannin sun kuma yi kira ga Moscow da ta kyale 'yan kasar Ukraine da aka tilastawa zuwa komawa gida nan take cikin aminci.

Belarus

Gungun kasashe masu arziki ya nuna matukar damuwarsa kan shirin da Rasha ke yi na isar da makamai masu linzami da za su iya daukar nukiliya zuwa Belarus a watanni masu zuwa.

Majiyar G7 ta ce, Zelensky ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su yi iyakacin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen mamayar da Rasha ke yi wa kasarsa a karshen wannan shekara, domin yanayin yaki zai kara tsanani ga dakarunsa yayin da suke kokarin kare kasarsu.

Masu kashe gobara na aiki bayan farmakin Rasha a wani yanki na Ukraine.
Masu kashe gobara na aiki bayan farmakin Rasha a wani yanki na Ukraine. AP - Nariman El-Mofty

Zelensky ya jaddada bukatar ci gaba da daukar tsauraran matakai kan Rasha, da kuma "kar a rage matsin lamba" duk da takunkumin da kasashen yammacin Turai suka dauka kan Moscow.

Tattaunawa

Ya ce bai shirya bude tattaunawa da Rasha ba, saboda har yanzu Kyiv na neman karfafa matsayinta, in ji fadar shugaban kasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.