Isa ga babban shafi

Ukraine ta ce Rasha na take-taken janyo Belarus cikin yakin da suke

Ma’aikatar tattara bayanan sirri na Ukraine tace Rashana kokarin janyo Belarus cikin aykin da ke wakana a tsakaninsu bayan da aka harba wasu makami masu linzami daga Belarus din zuwa iyakar arewacin Ukraine.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Faceboook, hukumarv ta ce an harba makamai masu linzami har guda 20 a wannan Asabar a kan kauyen Desna da ke yankin Chernigiv na arewacin kasar.

Ta kara da cewa makamai masu linzamin sun fada a wurare da ke arewacin birnin Kyiv da yankin Sumy, tana mai cewa ta gaano cewa Rasha na kokarin janyo Belarus cikin rikicin ne.

Luguden wutar na da karfi, sai dai babu wanda ya jikkata a sakamakonsu, a cewar hukumar  tattara bayanan sirrin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.