Isa ga babban shafi

Manyan kasashen G7 sun amince da haramta sayen zinare daga Rasha

A Lahadin nan manyan kasashen duniya suka amince da kudirin haramta sayen zinare daga kasar Rasha a yayin bude wani taron kungiyar G7, da zummar daukar matakan dankwafar da karfin Rasha a yakin da take da Ukraine.

Taron G7 a kasar Jamus.
Taron G7 a kasar Jamus. AP - Markus Schreiber
Talla

Shugabannin manyan kasashen wadanda ilahirinsu maza ne tun bayan saukar Angela Merkel daga mulkin kasar Jamus, su na neman hanyoyin kara taimaka wa Ukraine a yakin da take da Rasha ne, a yayin da suke fama da radadin tasirin da yakin ya  haifar.

Shugaban Amurka Joe biden da takwarorinsa daga akasarin kasashe masu karfin masana’antu sun gana a Jamus  kafin su garzaya birnin madrid don gudanar da taro da anokansu na kungiyar tsaro ta NATO.

A jawabinsa, shugaban Amurka Joe Biden ya ce takwaransa na Rasha Vladimir Putin ya yi fatan ganin kungiyatr tsaro ta NATO ta ruguje, amma hakan bata samu a gare shi ba.

A daya bangaren kuma Rasha ta ce dakarunta sun kai hari  a kan wasu cibiyoyin soji 3 a arewaci da yammacin Ukraine, har da guda a kusa da iyakar kasar da Poland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.