Isa ga babban shafi

Faransa: 'Yan sanda sun cafke mutane a zanga-zangar kare muhalli

Katafaren kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Faransa TotalEnergies ya kare kansa bayan da 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa a wajen taron shekara-shekara na masu rajin kare muhalli birnin Paris, bayan da gwamnatin kasar ta bukaci kamfanin da ya hanzarta sauya sheka zuwa makamashin da baya gurbata muhalli.

Masu rajin kare muhalli da ke zanga-zanga a birnin Paris.
Masu rajin kare muhalli da ke zanga-zanga a birnin Paris. REUTERS - STEPHANIE LECOCQ
Talla

Abin da rahotanni ke cewa shine, masu fafutukar kare muhalli sun yi zaman darshan a wurin da ake gudanar da wannan taro, ko da yake ‘yan sanda sun tsare mutum hudud aga cikinsu.

Da yake gabatar da jawabi a wurin taron, shugaban kamfanin Patrick Pouyanne y ace shirin yaki da matsalar diumamar yanayi, shine babban abin da suka sanya a gaba.

Ya ce, kamfanin nasa ya yi fiye da sauran takwarorinsa wajen saka hannun jarin da za a samar da shirin amfani da makamashin da baya gurbata muhalli.

A baya ‘yan sandan Faransa sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ke zaune a gaban wurin taron, bayan sun yi watsi da gargadin da aka yi musu na su fice daga wurin.

Pouyanne ya ce ya yi nadamar daukar matakai na musamman wajen kiran 'yan sanda domin hana masu zanga-zanga bayyana ra’ayoyinsu.

Masu zanga-zangar sama da 200 ne suka yi zaman darshan akan tituna, duk da cewa ‘yan sanda sun yi shirin ko ta kwana a kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.