Faransa ta kwashe daruruwan mutane daga gidajensu saboda gobarar daji
Hukumomin Faransa sukace an kwashe karin daruruwan mutane daga gidajensu yayin da gobarar daji ke ci gaba da ruruwa a kudu maso yammacin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Fiye da ma'aikatan kashe gobara 1,000, tare da tallafin jiragen sama masu zuban ruwan tara ke fafatawa tun ranar Talata don shawo kan gobarar biyu da tsananin zafi da yanayin iska mai karfi suka haddasa.
Hukumomin Gironde, inda gobarar ke ci gaba da ruruwa suka lamarin na kara kamari.
Yanzu haka ta lakume sama da hekta dubu 7, wato karin hekta 2,000 a cikin dare guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu