Isa ga babban shafi

Tattaunawa da China na da muhimmaci don kauce wa rikici - Amurka

Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce tattaunawa tsakanin Amurka da China na da matukar muhimmanci don kaucewa afkawa cikin rikici, bayan da Beijing ta yi watsi da wata ganawa tsakaninsa da takwaransa na China.

Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin.02/06/23
Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin.02/06/23 REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

Austin da Li Shangfu sun yi musafaha tare da takaitaccen jawabi a karon farko, yayin liyafar cin abincin dare na bude babban taron tsaro na Shangri-La a Singapore a, sai dai tattaunawarsu bata kai yadda ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ke bukatar ganin anyi ba kan musayar ra'ayi.

Babban hafsan tsaron na Amurka yana wani rangadi a yankin Asiya wanda a baya ya kai shi Japan kuma zai kai Indiya, a wani bangare na yunkurin da manyan jami'an Amurka ke yi na kulla kawance da hadin gwiwa a yankin don gogayya da Beijing.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.