Isa ga babban shafi

China ta gargadi Taiwan a kan ganawa da kakakin majalisar dokokin Amurka

China ta sha alwashin daukar mataki idan har shugabar Taiwan,  Tsai Ing-wen ta gana da shugaban majalisar dokokin Amurka a yayin ziyarar da ta ke a Washington.

Shugaban China,  Xi Jinping.
Shugaban China, Xi Jinping. via REUTERS - SPUTNIK
Talla

A wannan Larabar shugaba Tsai ta bar Taiwan zuwa Amurka, inda daga nan ne za ta dangana zuwa  Guatemala da Belize da zummar yaukaka dangantakar diflomasiyya da kawayen nata.

A kan hanyarta ta dawowa ne za ta  yada zango a jihar California, inda shugaban majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy ya bayyana aniyar ganawa da ita.

Har yanzu China tana daukar yankin Taiwan a matsayin wani bangare na kasarta, wanda za ta iya karbewa a kowane lokaci daga yanzu, kuma a karkashin manufarta ta ‘’One China’’, ba ta amince wata kasa ta kulla dangantaka da  yankin ba.

A wannan Laraba,  China ta fito filin ta bayyana rashin amincewarta da duk wata ganawa tsakanin Tsai da McCarthy, inda ta sha alwashin daukar matakin martani mai zafi.

Baya ga Guatemala da Belize, Taiwan tana da dangantaka da wasu kasashe a yankin Latin Amurka da Caribbean, ciki har da Paraguay da Haiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.