Isa ga babban shafi

Biden ya sha alwashin kare yankin Taiwan daga mamayar China

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce dakarun kasar za su kare Taiwan daga mamayar China, idan har kasar ta Sin ta yanke shawarar afkawa yankin da yaki.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. © AP - Evan Vucci
Talla

Ba wannan ne karo na farko da shugaban na Amurka ke furta cewa dakarun kasar za su shiga yaki tsakanin China da Taiwan ba, inda ya taba fadin haka a  watan Mayun da ya gabata, lokacin da ya ziyarci kasar Japan.

Yayin mayar da martani kan matsayin Amurka a Litinin din nan, China ta ce kalaman shugaba Joe Biden na cewa Amurka za ta kare Taiwan daga mamayar ta, ya saba wa manufar Washington game da tsibirin.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen China Mao Ning ya shaidawa wani taron manema labarai cewa, kalaman Joe Biden sun yi matukar cin karo da muhimmin alkawarin da Amurka ta dauka na kin goyon bayan 'yancin Taiwan.

A shekarar 1979, Amurka ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan, inda ta sauya sheka zuwa ga China. Sai dai Amurka ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa, wajen tallafawa yankin na Taiwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.